Ka dawo? – Buhari ya tambayi IGP yayinda sukayi Sallar Juma’a

Ka dawo? – Buhari ya tambayi IGP yayinda sukayi Sallar Juma’a

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a 18, ga watan Mayu, ya je masallacin Aso Rock domin gudanar da sallar juma’a tare da daruruwan al’ummar musulmi

- Shugaban kasar sunje masallacin tare da shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i

- Shugaba Buhari lokacin da suke gaisawa da Idris bayan sallar juma’a sai ya tambayarsa ashe ya dawo aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a 18, ga watan Mayu, ya je masallacin Aso Rock domin gudanar da sallar juma’a tare da daruruwan al’ummar musulmi.

Shugaban kasar sunje masallacin tare da shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i.

Shugaba Buhari lokacin da suke gaisawa da Idris bayan sallar juma’a sai ya tambayarsa ashe ya dawo aiki.

Ka dawo? – Buhari ya tambayi IGP yayinda sukayi Sallar Juma’a

Ka dawo? – Buhari ya tambayi IGP yayinda sukayi Sallar Juma’a

A ranar 9 ga watan Mayu majalisa ta jefa kuri’ar rashin tabbaci ga shugaban hukumar ta ‘Yan Sanda, inda ta bayyana shi a matsayin makiyin mulkin farar hula, bisa ga kin amsa gayyatar da majalisar tayi masa har sau biyu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

Limamin masallacin na Aso Rock Villa, a birnin tarayya, Abdulwaheed Abubakar, yayi godiya ga Allah bisa ga yadda ya bawa shugaban kasar namu lafiya da karfin jiki, ya kuma roki ubangiji ya kuma cigaba da kareshi ya bashi ikon tafiyar da aikinsa lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel