Boko Haram: Rundunar Sojin Kasa ta salwantar da rayukan 'Yan ta'adda 2, 11 sun shiga hannu

Boko Haram: Rundunar Sojin Kasa ta salwantar da rayukan 'Yan ta'adda 2, 11 sun shiga hannu

Mun samu rahoton cewa, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta samu nasarar salwantar da rayukan wasu 'yan ta'adda biyu na Boko Haram tare da cafke 11 yayin da ta farma maboyar su dake kauyukan Bukar Maryam da Abaganaram a jihar Borno.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, hukumar ta samu wannan nasara ne yayin artabu da 'yan ta'addan a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mataimakin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Onyeama Nwachukwu, shine ya fitar da wannan jawabi yayin ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.

Boko Haram: Rundunar Sojin Kasa ta salwantar da rayukan 'Yan ta'adda 2, 11 sun shiga hannu

Boko Haram: Rundunar Sojin Kasa ta salwantar da rayukan 'Yan ta'adda 2, 11 sun shiga hannu

Nwachukwu ya ci gaba da cewa, rundunar sojin ta samu wannan nasara ne tare da hadin gwiwar dakarun soji na kasar Kamaru da kuma rundunar hadin kai ta farar hula.

KARANTA KUMA: Shugabannin APC sun bukaci a sallami gwamnan Jihar Imo daga jam'iyyar

Legit.ng ta fahimci cewa, jarumtar da dakaru suka nuna yayin wannan artabu ya sanya suka samu nasarar kashe biyu daga cikin 'yan ta'addan tare da cafke 11 a yayin da suke yunkurin arcewa zuwa wasu kauyukan na kurkusa.

Ya kara da cewa, rundunar sojin ta kuma samu nasarar warware wasu bama-bamai inda kwato wasu muggan makamai na kare dangi daga hannun 'yan ta'addan tare da wasu babura 3 da kuma kakin soji guda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel