Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

- Ngozi Okonjo-Iweala wadda tayi minister har sau biyu ta bayyana dalilin da yasa bata ajiye aiki ba lokacin gwamnatin Jonathan duk da kiran da akayi ta mata na ta ajiye aiki

- A lokacin da take jawabi a makarantar koyon tattali da kimiyya a siyasa Iweala, tace ajiye aikin itace hanyar fita mafi sauki a lokacin wadda kuma bata shirya bin wannan hanya ba

- Ta shawarci matasa gwanaye kan yanda za su yi aiki a gwamnati irinta Najeriya, tsohuwar manajan daraktar bankin duniya tace dagewa da kuma goyon bayan ‘yan uwa da kuma kwarewa a gudanar da aiki sune suka sanya ta dade anayi da ita

Ngozi Okonjo-Iweala wadda tayi minister har sau biyu ta bayyana dalilin da yasa bata ajiye aiki ba lokacin gwamnatin Jonathan duk da kiran da akayi ta mata na ta ajiye aiki.

A lokacin da take jawabi a makarantar koyon tattali da kimiyya a siyasa a garin London, Iweala, tace ajiye aikin itace hanyar fita mafi sauki a lokacin wadda kuma bata shirya bin wannan hanya ba.

Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

Dalilin da yasa ban aje aiki a gwamnatin Jonathan ba - Okonjo-Iweala

Ta shawarci matasa gwanaye kan yanda zasuyi aiki a gwamnati irinta Najeriya, tsohuwar manajan daraktar bankin duniya tace dagiya da kuma goyon bayan ‘yan uwa da kuma kwarewa a gudanar da aiki sune suka sanya ta dade anayi da ita.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe

Ministar mai shekaru 63 wadda aka matsa kan ta ajiye aiki, tace ta shiga damuwa sanin cewa bazata iya magance matsalar da kasar ke fuskanta ba, amma dai ta san cewa zatayi iyaka gwargwadon kokarin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel