Shugaba Buhari ya bayyana abinda Jihar Ekiti ta rasa Karkashin gwamna Fayose

Shugaba Buhari ya bayyana abinda Jihar Ekiti ta rasa Karkashin gwamna Fayose

Mun samu rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fashin baki dangane da hali na yanayi da al'ummar jihar Ekiti suka shiga karkashin jagorancin gwamnan jihar, Ayodele Fayose.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, aminci da daidaito da aka san al'ummar jihar tuni sun shiga rububi da a yanzu an nema an rasa karkashin gwamnatin Fayose.

Shugaba Buhari ya bayyana abinda Jihar Ekiti ta rasa Karkashin gwamna Fayose

Shugaba Buhari ya bayyana abinda Jihar Ekiti ta rasa Karkashin gwamna Fayose

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Post sun bayyana cewa, shugaba Buhari yayi wannan hasashe ne da fashin baki yayin karbar bakuncin jiga-jigan jam'iyyar na yankin Kudu maso Yammacin kasar nan yayin da suka ziyarce shi a fadar sa ta Villa dake garin Abuja.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Shekara 58 ya yiwa 'Yar Shekara 12 Fyade a jihar Edo

Shugaba Buhari yake cewa, lokaci yayi da ya kamata jam'iyyar APC ta dawo da wannan martaba ta mutunci da darajoji masu nagarta da aka rasa a jam'iyyar da zasu dawo da martabar jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya yi wannan hasashe na dawo da martabar sakamakon nasarar da jam'iyyar APC tayi wajen fitar da dan takarar gwamna na jihar, inda Ministan ma'adanan Kasa Mista Kayode Fayemi da ya zamto zakara a zaben da aka gudanar a makonnin da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel