Shugabannin APC sun bukaci a sallami gwamnan Jihar Imo daga jam'iyyar

Shugabannin APC sun bukaci a sallami gwamnan Jihar Imo daga jam'iyyar

Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Imo ya dauki wani sabon salo a ranar Alhamis din da ta gabata, inda jiga-jigan jam'iyyar na jihar suka kirayi shugaban jam'iyyar na kasa baki daya, Cif John Odigie-Oyegun, akan ya kori gwamna Rochas Okorocha daga jam'iyyar.

Wannan kira yazo ne da sanadin Sanatoci masu wakiltar jihar a majalisar dattawa da suka hadar da; Ifeanyi Ararume, Hope Uzodimi, Osita Izunaso da sauran jiga-jigai na jam'iyyar.

Masu ruwa da tsaki cikin korafin ga shugaban jam'iyyar na kasancewa, muddin jam'iyyar tana mararin samun nasara cikin yankunan Kudu Maso Gabashin kasar nan a zaben 2019 to kuwa sai ta tsarkake kanta daga tarayya da gwamna Okorocha.

Shugabannin APC sun bukaci a sallami gwamnan Jihar Imo daga jam'iyyar

Shugabannin APC sun bukaci a sallami gwamnan Jihar Imo daga jam'iyyar

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin wata rubutacciyar wasika da jiga-jigan jam'iyyar suka aikawa shugaban ta na kasa, sun bayyana cewa ya kamata ayi watsi da gwamna Okorocha tun kafin rawar da yake takawa a halin yanzu ta kawo barazana da zamto annoba ga jam'iyyar baki daya.

KARANTA KUMA: Birnin Gwari: Rayuka 8 sun salwanta a wani Hari na Sanyin Safiya

Jiga-jigan jam'iyyat sun yi hasashen cewa muddin ana neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Imo, to kuwa sai tayo watsi da gwamnan jihar da a yanzu ya zamto dafi da ka iya harbin jihar da zai sanya dokar ta baci da sashe na 305 cikin kundin tsarin mulki ya yi tasiri.

A yayin haka kuma, jiga-jigan jam'iyyar sun yi godiya da jinjina ga shugaban jam'iyyar na kasa dangane da jajircewa da tsayuwar daka wajen assasa dokoki da tsare-tsare da suka kawo nasara ta gudanar da gangamin ta a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel