Sanatan APC ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Jam’iyya

Sanatan APC ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Jam’iyya

- Sanata Kabiru Marafa ya koka da rashin bin doka a Jam’iyyar APC

- ‘Dan Majalisar ya nemi Shugaba Buhari yayi wani abu kan rikicin

- Sanatan na APC yace idan aka yi wasa Jam’iyyar na iya fadi zabe

Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Marafa mai wakiltar Yankin Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar APC ya nemi Shugaban kasa Buhari da kan sa yayi wani abu game da rikicin Jam’iyyar.

Sanata Kabiru Marafa ya nemi Shugaban kasar da kan sa ya kawo karshen rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar inda yace idan aka yi sake rikicin na iya cin Jam’iyyar a zabe mai zuwa na 2019. Ba dai Sanatan ba ne ya fara kokawa a APC.

Kabiru Marafa wanda shi ne Shugaban Kwamitin harkar man fetur a Majalisar Dattawa ya soki yadda aka gudanar da zaben shugabanni a Jihar Zamfara. Sanatan ya zargi Gwamnan Jihar Abdulaziz Yari da saba dokar Jam’iyyar.

Sanatan dai yace an yi kutun-kutun ne a zaben da aka yi kwanan nan kuma Shugaban kasar na iya samun kan sa cikin matsala. ‘Dan Majalisar ya soki yadda wasu su kayi kokarin karawa Shugabannin Jam’iyyar wa’adin shekara guda.

‘Dan Majalisar dai yayi wannan bayani ne a gaban manema labarai a Garin Abuja inda ya gargadi Shugaban kasar yayi wani abu tun kafin APC ta sha kasa a zaben 2019. Shugaba Buhari dai yace baya shiga cikin lamarin Jam’iyya domin ba aikin sa bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel