2019: Akwai makirci da ake shiryawa na doke shugaba Buhari daga kujerarsa - Sanata Marafa

2019: Akwai makirci da ake shiryawa na doke shugaba Buhari daga kujerarsa - Sanata Marafa

- Sanata kabir Marafa yayi ikirarin cewa ana shawarwarin doke shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a zaben 2019

- Shugaban kasar wanda ya bayyana kudurinsa na sake tsayawa takara 2019 a ranar Litini, 9 ga watan Afirilu

- Marafa ya bayyana cewa akwai wasu cikin shuwagabannin jam’iyyar wadanda sukayi yunkurin kawo hargitsi a wurin taron da aka gudanar a jihar Zamfara a cikin ‘yan kwanakin nan

Sanata kabir Marafa, mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, yayi ikirarin cewa ana shawarwarin doke shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a zaben 2019.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sanata Marafa wanda shine ciyaman na kwamitin kula da man fetur a majalisa yace an watsa masa barkonon tsohuwa a wurin taron da magoya bayansa suka gudanar a garin Zamfara a ranar Asabar, 12 ga watan Mayu.

2019: Akwai makirci da ake shiryawa na doke shugaba Buhari daga kujerarsa - Sanata Marafa

2019: Akwai makirci da ake shiryawa na doke shugaba Buhari daga kujerarsa - Sanata Marafa

Marafa ya bayyana cewa akwai wasu cikin shuwagabannin jam’iyyar wadanda sukayi yunkurin kawo hargitsi a wurin taron da aka gudanar a jihar Zamfara a cikin ‘yan kwanakinnan.

KU KARANTA KUMA: Da zaran ka koma jam’iyyar Buhari toh ka zama tsarkakakke - Wike

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Buhari ya bayyana kudurinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019 a ranar Litinin, 9 ga watan Afirilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel