Gwamnonin Arewa za su kori Ma’aikatan Makaranta a 2019 – El-Rufai

Gwamnonin Arewa za su kori Ma’aikatan Makaranta a 2019 – El-Rufai

- Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai yace bayan 2019 Gwamnoni za su gyara harkar ilmi

- Mal Nasir El-Rufai yake cewa gudun faduwa zabe ya sa wasu ke gudun taba harkar ilmi

- Gwamnan yace ba ya shakkar daukar wani mataki da zai taimakawa al’ummar Kaduna

Mun samu labari cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Gwamnonin Jihohin Arewa za su sallami wasu bara-gurmin Malaman Makaranta idan su ka lashe zabe a 2019.

Gwamnonin Arewa za su kori Ma’aikatan Makaranta a 2019 – El-Rufai

Gwamna El-Rufai yace bai tsoron rasa kujerar sa

Gwamna Malam Nasir El-Rufai yace Gwamnonin Arewan na gudun rasa kujerar su ne a zabe mai zuwa shi ya sa su ka gaza korar Ma’aikatan da ba su san aiki ba. El-Rufai yayi wannan bayani ne lokacin da yake wani jawabi kwanan nan.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bayan zaben 2019 Gwamnonin Arewa da dama za su kori Malaman Makaranta kamar yadda yayi a Jihar Kaduna kwanakin baya. Gwamnan na APC yace abin da su ka yin yayi daidai.

KU KARANTA: Dangote zai kafa kamfanin kera motoci a Arewacin Najeriya

El-Rufai yayi wannan jawabi ne a wata Makarantar koyon aikin Likita a Jihar Ondo. Gwamnan na Kaduna yake cewa Gwamnonin kasar da dama sun yaba masa bayan ya kori Malaman makaranta sama da 20, 000 da su ka fadi jarrabawa.

Nasir El-Rufai ba ya jin tsoron daukar kowane irin mataki a Duniya idan har ya ga cewa shi ne abin da ya dace. Malam El-Rufai yace sauran Gwamnonin Kasar ba za su iya yin gangancin da yayi ba saboda gudun za su fadi zabe a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel