Da zaran ka koma jam’iyyar Buhari toh ka zama tsarkakakke - Wike

Da zaran ka koma jam’iyyar Buhari toh ka zama tsarkakakke - Wike

- Gwamna Nyesom Wike ya zargi jam’iyyar adawa wadda ke kan mulki da nuna son kai ta fannin yaki da rashawa a Najeriya

- Wike yace yakin da gwamnatin mai mulki ta APC takeyi ba wani abu bane illa siyasa

- Gwamnan yace ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin APC jira kawai sukeyi 2019 tayi su cire ta daga kan mulki

Gwamna Nyesom Wike ya zargi jam’iyyar adawa wadda ke kan mulki da nuna son kai ta fannin yaki da rashawa a Najeriya, saboda haka yake kira ga ‘yan Najeriya dasu hada hannu wurin marawa PDP baya a shekarar 2019.

Wike yace yakin da gwamnatin mai mulki ta APC, takeyi ba wani abu bane illa siyasa, ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da aka yada a yanar gizo inda yace APC mayaudara ne kawai.

Da zaran ka koma jam’iyyar Buhari toh ka zama tsarkakakke - Wike

Da zaran ka koma jam’iyyar Buhari toh ka zama tsarkakakke - Wike

Gwamnan yace ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin da kuma karairayin da APC takeyi musu tun hawansu mulki 2015, saboda haka jira kawai sukeyi 2019 tayi su cire ta daga kan mulki.

KU KARANTA KUMA: Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya Kabiru Marafa, yayi ikirarin cewa wasu cikin manyan ‘yan siyasa a Najeriya suna kokarin sauke shugaba Buhari daga bisa mulki a shekarar 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel