Makasan da aka damke sun bayyana Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara a matsayin masu daukan nauyinsu

Makasan da aka damke sun bayyana Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara a matsayin masu daukan nauyinsu

Makasan da hukumar yan sandan jihar Kwara ta damke makon da ya gabata sun bayyana sunan shugaba majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed, a matsayin masu basu umurnin kashe mutane.

Bisa ga rahoton da Sahara Reporters ta samu, Yan bindigan wadanda aka kawo Abuja domin bincike sun ambaci sunayen wadannan yan siyasa a asirin da suka tona.

Game da jawabin da suka yiwa yan sanda, yan bindigan sunce sun kasance gwamnatin jihar da ofishin Saraki na biyansu albashi kowani wata.

Makasan da aka damke sun bayyana Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara a matsayin masu daukan nauyinsu

Makasan da aka damke sun bayyana Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara a matsayin masu daukan nauyinsu

Shugaban makasan, wanda yaron Salihu Woru ne ya kasance kan albashin dirakta a gwamnati, kuma sauran na matsayin sama da na mai digiri.

Bugu da kari, makasan sun bayyana cewa ana biyansu daga ofishin shugaban majalisan dattawa, kuma an basu motoci kirar Toyota Corolla domin zaben 2019.

Daga cikin jerin wadanda akace su kashe sune; Mustapha; Kayode Oyin, Yinka Aluko, Baba Rex, da Ogunlowo.

Wani majiyan yan sanda ya bayyanawa Sahara Reporters cewa an samu takardan banki wanda ke nuna cewa suna karban kudi daga hannun Saraki da gwamnatin jihar Kwara.

Wannan shi yasa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi bayani a zauren majalisa cewa sifeto janar na kokarin kulla masa sharri na alakantashi da wasu yan bindiga da aka kama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel