Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

Shahararren attajirin dan kasuwan nan kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ziyarci jihar Niger a ranar Alhamis, 17 ga watan Mayu.

Attajirin ya ziyarci garin Minna ne tare da ‘yar sa Halima, da kuma mijin ta Bello Suleiman, da kuma wasu ma’aikatan kamfanin Dangote.

Sun je garin Minna babban birnin jihar ta Niger ne domin halartar taron raba kayan agaji na Naira milyan 250 da Gidauniyar Dangote ta baiwa mata masu karamin karfi har su dubu 25.

Daga wajen taron Dangote ya yada zang a gidan tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida inda ya shafe awa daya a cikin gidan.

Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

Bayan fitowar sa dai bai shaida wa manema labarai abin da suka tattauna ba.

KU KARANTA KUMA: Shehu yace an samu zaman lafiya yanzu a Borno

Cikin wadanda suka take masa baya zuwa gidan Babangida har da Gwamnan Jihar, Abubakar Bello, Sanata Bala Ibn Na’Allah da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jiha, Mikail Bmitosashi.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa attajirin ya sake shiga jerin masu kudin duniya, inda ya kasance mutun daya dilo da ya samu shiga rukunin a nahiyar Afrika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel