Wasu makasa sun ce Saraki da gwamnan Kwara ne iyayen gidansu

Wasu makasa sun ce Saraki da gwamnan Kwara ne iyayen gidansu

- Siyasar Kwara ta dauki dumi bayan da IGP ke zargin na uku a Najeriya da daukar nauyin yan ta'adda

- Manyan biyu sun karyata zargin tun kafin aje kotu

- Bukola Saraki ya kai wa shugaban kasa kara

Wasu makasa sun ce Saraki da gwamnan Kwara ne iyayen gidansu

Wasu makasa sun ce Saraki da gwamnan Kwara ne iyayen gidansu

Wasu wadanda ake zargi da kashe kashe da hukumar 'yan sandan jihar Kwara ta kama su a satin da ya gabata sun ambaci shugaban majalisar dattawa, Mista Bukola Saraki da Gwamnan jihar Kwara, Mista Abdulfattah Ahmed, a matsayin mutanen da suka umarce su da kashe mutanen jihar Kwara.

Tuni da aka kai wadanda ake zargi Abuja don cigaba da bincike.

Kamar yanda wadanda ake zargin suka cewa 'yan sandan, Gwamnatin jihar Kwara ce ta biyasu tare da ofishin Mista Saraki.

Shugaban makasan, Dan salihu woru, wanda ke magana da yawun Magajin Masarautar Ilorin, an dorashi a matsayin matakin albashi na 16,sauran kuma daga mataki na 10 zuwa 15.

A rahoton da Sahara Reporters suka tattara sunce, ana biyansu ne ta ofishin shugaban majalisa, Mista Bukola Saraki, kuma shi ya basu motoci kirar Toyota Corolla watanni kadan da suka gabata domin tanadin zaben 2019 dake gabatowa.

Wata majiya daga hukumar 'yan sanda tace an samesu da shaidar banki mai nuna cewa suna karbar albashi duk wata daga Saraki da kuma Gwamnatin jihar Kwara. An gane cewa asusun su na banki shaqe yake da miliyoyin Nairori.

DUBA WANNAN: Kashe-kashen da ake ba na kabilanci ko addinanci bane

Bayan wadanda ake zargin sun yi tonon silili ne Bukola Saraki da Ahmed suka nemi hurawa kwamishinan .yan sandan jihar Kwara, Mista Aminu Pai Saleh wuta, ta karkashin DPP, Mista Jimoh Mumini, wanda ake ce ya Kware a cin rashawa.

Ance an ba Mista Pai Saleh kudi, amma yaki karba. Daga nan ya maida wadanda ake zargin Abuja.

Akwai dai yuwawar gayyato Mista Bukola da Ahmed don amsawa 'yan sanda tambayoyi.

Su biyun dai sun zargi shugaban 'yan sanda, Mista Ibrahim Idris da shirin liqa musu laifin kisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel