Makaman Makiyaya: Abin da Buhari ke nufi kan zargin Ghaddafi da yayi - Ministan Tsaro

Makaman Makiyaya: Abin da Buhari ke nufi kan zargin Ghaddafi da yayi - Ministan Tsaro

- Shugaba Buhari ya alakanta Ghaddafi marigayi da yaduwar makamai a Sahel

- Wasu na ganin gazawar gwamnatin Tarayya kan kashe-kashen makiyaya

- Kashe-kashen tsakiyar Najeriya sun kai laa-haula

Makaman Makiyaya: Abin da Buhari ke nufi kan zargin Ghaddafi da yayi - Minista

Makaman Makiyaya: Abin da Buhari ke nufi kan zargin Ghaddafi da yayi - Minista

Gwamnatin tarayya ta dorawa hanyoyin shiga da fice na hamada laifin yaduwar makamai, sakamakon hargitsin kasar Libya.

A wani taro da akayi a Abuja, a ranar Alhamis, Ministan tsaro, Dan Ali, yayi magana akan matsalar da ake samu ta makiyaya da manoma.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya bada misali da horar da makiyaya da ake a kasar Libya shi yake kawo samuwar makamai, wanda ke kawo asarar rayuka da dama.

Ya kara bayyana cewa gwamnati ta hada kwamitin da zai duba yanda ake shigo da makamai kuma ya tilastawa National Emergency Management Authority (NEMA) da ta sake gina kauyuka a jihar Benue, tare da tabbatar da cewa basu da nisa da juna.

Mista Dan Ali yayi koke da cewa yawan sojojin kasar bazai isa duk kauyukan tsakiyar kasar ba.

Taron wanda ma'aikatar labarai da al'adu ta shirya ya samu halartar, Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, Ministan noma da raya karkara, Audu Ogbeh da ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau.

DUBA WANNAN: Kashe-kashen da ake ba na kabilanci ko addinanci bane

Mista Dambazau yace yaduwar makamai a kasar Libya ba ita kadai ya shafa ba ita da Najeriya. Amma dukkan kasashen Afirka ta yamma.

Mista Ogbeh a jawabin shi yace kamar yanda kasar Argentina, Pakistan da Namibia suke shirin samar da wutar lantarki daga kashin shanu, Gwamnatin ce ta tallafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel