Shehu yace an samu zaman lafiya yanzu a Borno

Shehu yace an samu zaman lafiya yanzu a Borno

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Al-Kami, ya bayyana cewa an samu zaman lafiya a jihar yanzu ta yadda kowa zai iya gabatar da harkokin gabansa.

Basaraken na jawabi ne ga jami’an hukumar bayar da agaji dake Kaduna wato Arrida Relief Foundation of Nigeria (ARFON), karkashin jagorancin shugabanta, Hajiya Rabi Salisu Ibraheem, a lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma.

“Wasu ne suka kawo Boko Haram daga wani waje,” ya kara da cewa “Mohammed Yusuf (ma’assashin kungiyar) da Ibrahim Shekau sun zo Borno daga wani waje ne domin neman ilimin Qur’ani da na zamani, ba tare da mutane sun cewa suna da wata boyayyar manufa ba."

Shehu yace an samu zaman lafiya yanzu a Borno

Shehu yace an samu zaman lafiya yanzu a Borno

Shehu wanda a take aka daura shi a matsayin uban kungiyar a jihar Borno, ya bayyana cewa masarautar Borno zatayi aiki tare da su domin tallafawa marayu, zawarawa da al’umma daga bangarensu.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC na daf da yin wani babban rashi a Kudancin Najeriya Jam’iyyar APC na daf da yin wani babban rashi a Kudancin Najeriya

Hajiya Rabi Salisu Ibrahim, tace kungiyar zata dauki nauyin marayu 66 da zawarawa 3450 da harin Boko Haram ya shafa a Kaduna.

Tace akwai jami’ai a Borno da zasu hada wasu yara da take kulawa da su ga iyayensu da aka gano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel