Wani 'Dan Shekara 58 ya yiwa 'Yar Shekara 12 Fyade a jihar Edo

Wani 'Dan Shekara 58 ya yiwa 'Yar Shekara 12 Fyade a jihar Edo

Mun samu rahoton cewa wani Bawan Allah dan kimanin shekaru 58 a duniya, ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda a babban birnin Benin na jihar Edo bisa laifin yiwa wata dalaibar sa fyade wadda ba ta wuci shekaru 12 a duniya ba.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, jagoran cibiyar ilimi na jihar, Dakta Joan Oviawe, ita ce ta yi korafin wannan lamari ga hukumar 'yan sanda kafin a damke mutumin da ake zargi da wannan aika-aika.

Dakta Oviawe ta shaidawa manema labarai cewa, yawaitar fashi da dalibar ke yi ne ya sanya akan binciki lamarin inda ta kwashewa malamin ajin su labarain yadda wani mutum mai sunan Lambert Ighodaro ya yaudare ta wajen biyan bukatar sa ta dan namiji.

Wani 'Dan Shekara 58 ya yiwa 'Yar Shekara 12 Fyade a jihar Edo

Wani 'Dan Shekara 58 ya yiwa 'Yar Shekara 12 Fyade a jihar Edo

Legit.ng ta fahimci cewa, Lambert dai ya samu nasarar aikata lalata da wannan daliba a gidan sa tun a shekarar da ta gabata, inda daga bisani ya danka mata wasu 'yan kudade domin ta kame bakin ta.

KARANTA KUMA: Anyi Arangama tsakanin Hukumar Kastam da 'Yan Sumoga, ta ritsa da wani 'Dalibi

A halin yanzu Dakta Oviawe ta bayyana cewa, cibiyar ta na kuma ci gaba da gudanar da bincike wasu laifuka na lalata kan kananun yara da suka afku a makarantu.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Babatunde Johnson Kokumo, ya tabbatar da wannan lamarin inda ya bayyana cewa tuni Mista Lambert ya shiga hannun hukuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel