Babu yadda za ayi NNPC tace ana shan lita miliyan 600 na fetur kullum - Yari

Babu yadda za ayi NNPC tace ana shan lita miliyan 600 na fetur kullum - Yari

Gwamnonin Najeriya sun koka da yadda Hukumar NNPC ta daga yawan adadin Man fetur da ake sha a kowace raba a kasar. Gwamnonin kasar sun kuma nemi a binciki lamarin tallafin man fetur.

A jiya ne aka yi taron Majalisar tattalin arzikin kasar inda Gwamnonin Jihohi su ka zargi Hukumar NNPC da karkatar da kudin tallafin man fetur. Shugaban Gwamnonin Kasar Abdulaziz Yari ya bayyana wannan bayan taron na jiya.

Babu yadda za ayi NNPC tace ana shan lita miliyan 600 na fetur kullum - Yari

Gwamnoni ba su yarda da lissafin NNPC na jigilar mai ba

Abdulaziz Yari yace watanni kadan da su ka wuce Najeriya na shan lita miliyan 30 ne na fetur a rana. Sai dai kuma bayan gangar mai ya tashi a Duniya sai NNPC ta koma cewa a duk rana ta Allah ana amfani da lita miliyan 60 a kasar

KU KARANTA: Kasar Amurka ta kira Shugaba Buhari a wayar tarho

Gwamnan na Zamfara ya fadawa Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo cewa da-walakin a lamarin na NNPC kuma sam ba za su yarda da wannan danyen aiki ba. Yari yace man da NNPC ta ke ikirari ana amfani da shi yayi yawa.

A cewar Gwamnan babu yadda za ayi NNPC ta ce ana shigo da lita miliyan 60 Najeriya ko da kuwa Kasar nan ke ba Makwabta man fetur. Gwamna Yari yace su na gudun a maimaita abin da ya faru a 2015 a Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari.

Gwamnonin dai sun nemi NNPC ta rika harkokin ta dalla-dalla domin gudun a rasa inda wasu kudi su ka shiga. Gwamnoni irin su Udom Emmanuel, Godwin Obaseki, Seriake Dickson da Nasir El-Rufai da kuma Atiku Bagudu su ka halarci taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel