Shugaban Amurka Trump dakiki ne, cewar Bill Gates mai kudin duniya

Shugaban Amurka Trump dakiki ne, cewar Bill Gates mai kudin duniya

- Shugaban Amurka yana shan suka daga manyan siyasar Amurka

- Yawanci yakan mayar da martani cikin fushi kuma ya hakikance shine kan daidai

- A yanzu mai kudin duniya ne ya tsokalo shi

Shugaban Amurka Trump dakiki ne, cewar Bill Gates mai kudin duniya

Shugaban Amurka Trump dakiki ne, cewar Bill Gates mai kudin duniya

A hirarsa da wani gidan talabijin na jarida a Amurka, yayin bada gudummawar dala miliyan 12 don yakar cutar kanjamau HIV a fadin kasar Amurka, Bill Gartes, yace shugaban Amurka Trump bai ma san banbancin cutukan HIV da HPV ba.

A cewarsa, a ganawarsu ta baya-bayan nan a bara, ya gano cewa shugaban Amurka bai san banbancin ma kanjamau da papiloma virus ba.

Dama dai Amurkawa da yawa na ganin wallar shhugaban nasu Donald Trump, wanda da yawa wadanda suka zabe shi dama ba wani ilimin boko suka yi ba, sai dai suna da zazzafan kishin farar fata da ma addinin masihanci.

DUBA WANNAN: Anyi ganawar sirri da Buhari da Modu Sheriff

Shuagabannin Amurka a baya, sukan zo ne da ilimin boko gwargwado, shi kuwa Trump, yaci zabe ne da kuri da cika baki, da bambadanci da kanzagi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel