Rikicin makiyya bashi da alaka da addinanci, kabilanci - wai inji binciken gwamnantin Tarayya

Rikicin makiyya bashi da alaka da addinanci, kabilanci - wai inji binciken gwamnantin Tarayya

- A Najeriya, ana ta kashe kauyawa kamar banza

- Gwamnatin Tarayya ta tashi haikan wajen ganin ta magance kisan gillar

- An ganoo rikicin wai bashi da alaka da kabilanci

Rikicin makiyya bashi da alaka da addinanci, kabilanci - binciken gwamnantin Tarayya

Rikicin makiyya bashi da alaka da addinanci, kabilanci - binciken gwamnantin Tarayya

A taron karawa juna ahimta da gwamnatin Tarayya ta shorya inda ministocin ta ke shawagi jihohin da abinn ya shafa, sakamakon binciken gwamnatin ya nuna cewa wadannan karin kashe-kashe da ake yi a kasar nan wai bashi da alaka da addinanci ko kabilanci.

Alhaji Lai Muhammed, Ministan sadarwa ne ya bayyana hakan, a yayin zantawa da dattijai da abin ya shafi jihohin su.An kuma sami halartar shuwagabannin kabilu cikharda na makiyaya na Miyetti Allah.

A taron da tashar Channels ta nada, an sami halartar ministocin tsaro, cikin gida, bayanai da muhalli, sai na ruwa da kauyuka.

A cewar Mista Lai dai, koda yake wasu na son suce kashe-kashen suna da alaka da kisan kare dangi don addinanci da kabilanci, a'a, kisan kawai na wasu tsinannu ne da basu da tausayi, masu kuma son tada zaune tsaye.

DUBA WANNAN: Anyi ganawar sirri da Buhari da Sheriff

Kisan gillar dai ana yinsa ne a jihohin tsakiyar Najeriya, kuma an ffi zargin makiyaya da ake kira Fulani daga ketare da aikata su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel