Jam’iyyar APC na daf da yin wani babban rashi a Kudancin Najeriya

Jam’iyyar APC na daf da yin wani babban rashi a Kudancin Najeriya

- Rikicin APC na nema ya sa a rasa wani babban ‘Dan Majalisa

- Akwai kishin-kishin din cewa Sanatan Ribas Abe zai koma PDP

- Rigimar Sanatan da tsohon Gwamnan Jihar Ribas ta ki karewa

Mun samu labari cewa Jam’iyyar PDP na neman dauke wani Sanaran APC na Jihar Ribas. Yanzu dai har an fara rade-radin cewa Sanata Magnus Abe ya kama hanyar barin APC saboda rikicin Jam’iyyar.

Jam’iyyar APC na daf da yin wani babban rashi a Kudancin Najeriya

Watakila Sanata Magnus Abe ya bar APC ya koma PDP

Kamar yadda mu ka ji, Hadiman Sanatan Ribas na Kudu maso Gabas watau Magnus Abe da kuma manyan Mukarabban sa su na ta wani kus-kus da Gwamnan Jihar na Ribas Nyesom Wike a cikin gidan Gwamnati da ke Fatakwal.

Rikicin da ya barke a Jam’iyyar ta APC ne ya sa Sanata Magnus Abe ke kokarin komawa PDP wanda tun ba yau ba ake rade-radin cewa Sanatan zai sauya sheka. Wasu Yan APC kuma sun koka da cewa Abe ne ke kokarin kawo baraka.

KU KARANTA: Wasu manyan 'Yan APC sun koma SDP a Jihar Jigawa

Jam’iyyar dai tana ta samun kan-ta cikin rikici har kawo yanzu da aka yi zaben Shugabannin Kananan Hukumomi. Rigimar dai tsakanin Ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma Sanata Magnus Abe ta dade an gaza magance ta.

Kwanakin baya kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kudancin Najeriya Injiniya Segun Oni ya bayyana cewa idan aka yi sake fa zai tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar saboda banbancin da ake nunawa Magoya bayan sa a APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel