An yi haka-haka a zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2014 - Buhari

An yi haka-haka a zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2014 - Buhari

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammas Buhari yayi magana kan zaben Jihar Ekiti da aka yi a 2014 lokacin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan yana kan mulki. Ayo Fayose ne yayi nasara a zaben ya doke Kayode Fayemi.

An yi haka-haka a zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2014 - Buhari

Shugaba Buhari ya nemi APC ta karbe Jihar Ekiti a bana

Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da zaben 2014 da Ayo Fayose yayi nasara yana mai nuna takaicin sa da abin da ya faru a lokacin zaben. Shugaban kasar yayi nemi APC tayi bakin-kokari wajen yin nasara a zaben bana.

Jaridun Kasar nan sun rahoto cewa Shugaban kasar ya nuna takaicin sa ga zaben na 2014 yace an fada masa yadda aka yi, yana mai kira ga Shugabannin APC a Yankin da ka da su bari haka ta sake faruwa a zaben da za ayi wannan watan.

KU KARANTA: Wanda ke kokarin sasanta ‘Yan APC yana neman barin Jam’iyyar

Shugaba Buhari dai yace ya zare hannun sa daga shiga cikin lamarin Jam’iyya domin ba aikin sa bane. A makon jiya ne dai APC ta gudanar da zaben fitar da gwani inda Ministan kasar Kayode Fayemi ya samu tikitin takara a Jam’iyyar.

A wancan zaben dai ana zargin an yi amfani da Jami’an tsaro wajen murde kuri’un Jama’a. A haka ne dai Ayo Fayose yayi nasara. Yanzu dai za a kara ne tsakanin tsohon Gwamna Kayode Fayemi da kuma Mataimakin Gwamna Ayo Fayose.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel