Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi jakadojin kasashen Guinea-Bissau da Thailand

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi jakadojin kasashen Guinea-Bissau da Thailand

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a yau ya karbi takardun shaidar turowa daga jakadojin kasashen Guinea-Bissau da Thailand ranar Alhamis 17 ga watan Mayu a fadar sa dake a unguwar Aso Rock babban birnin tarayya Abuja.

Wadanda suka kai masa takardun jakadancin dai sune Mista Henrique Adriano Da Silva daga kasar Guinea-Bissau da kuma Mista Wattana Kunwongse na kasar Thailand.

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi jakadojin kasashen Guinea-Bissau da Thailand

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi jakadojin kasashen Guinea-Bissau da Thailand

KU KARANTA: Siyasa na neman lalata imanin Osinbajo - PDP

A wani labarin kuma, Hukumar nan mallakin gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta kama dan majalisar dattijai dake wakiltar al'ummar yankin jihar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas mai suna Sanata Bassey Akpan.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta EFCC ta kama Sanata Bassey Akpan ne bisa zargin karbar cin hancin motocin alfarma da suka kai darajar Naira miliyan 303 daga hannun wani hamshakin mai kudi Babajide Omokore da yanzu haka yake fuskantar shari'a.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel