Anyi Arangama tsakanin Hukumar Kastam da 'Yan Sumoga, ta ritsa da wani 'Dalibi

Anyi Arangama tsakanin Hukumar Kastam da 'Yan Sumoga, ta ritsa da wani 'Dalibi

Wani dalibin makarantar sakandire mai kimanin shekaru 17 a duniya, Isiaka Ganiyu, ya rasa ran sa yayin da hukumar kastam da dakarun soji suka yi arangama da wasu 'yan sumoga a garin Ilara dake karamar hukumar Afon ta jihar Ogun a karshen makon da ya gabata.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, kimanin rayuka uku ne suka salwanta yayin wannan arangama ta sassafiya da ta afku a ranar Asabar din da ta gabata.

Anyi Arangama tsakanin Hukumar Kastam da 'Yan Sumoga, ta ritsa da wani 'Dalibi

Anyi Arangama tsakanin Hukumar Kastam da 'Yan Sumoga, ta ritsa da wani 'Dalibi

Wannan dalibi dai ya gamu da azal ne inda aka raunata shi da harsashi yayin artabun, wanda ya sanya aka yi gaggawar garzayawa da shi asibiti na kurkusa dake gaba ta iyakar Najeriya da kasar Benin.

KARANTA KUMA: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana masu haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

Rahotanni sun bayyana cewa, Ganiyu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Talatar da ta gabata inda kuma aka yi jana'izar sa a ranar Laraba ta wannan mako.

A sakamakon wannan lamari ne ya sanya majalisar dokoki ta jihar Ogun ta gargadin hukumar kastam akan taka-tsan-tsan yayin gudanar da harkokin su na dakile fasakauri a yankunan dake gaba da jihar domin kiyaye afkuwar hakan a lokuta na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel