Allah ya yiwa shugaban wata jarida a Najeriya rasuwa

Allah ya yiwa shugaban wata jarida a Najeriya rasuwa

Allah ya yi babban direktan jaridar New Nigerian Newspapar rasuwa. Alhaji Tukur Abdulrahman ya rasu ne a daren jiya 17 ga watan Mayu a wata asibiti da ke Asokoro, Abuja bayan ya yi fama da ciwon zuciya.

Sanarwan da ta fito daga iyalan mamacin ta ce za'ayi jana'izar shi yau Juma'a 17 ga watan Mayu a garin Daura da ke jihar Katsina.

Kafin rasuwarsa Abdulrahman ya yi aiki a matsayin edita na 'Gaskiya ta fi kwabo' wadda ake wallafawa a jaridar ta New Najeriya.

Allah ya yi shugaban wata jarida a Najeriya rasuwa

Allah ya yi shugaban wata jarida a Najeriya rasuwa

Marigayin ya rasu ya bar mata guda daya da yara biyar.

Allah ya jikansa da Rahama. Amin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel