Kuma dai: Yan bindiga sun kashe mutum 4 sun banka ma gidaje wuta a garinsu Dino Melaye

Kuma dai: Yan bindiga sun kashe mutum 4 sun banka ma gidaje wuta a garinsu Dino Melaye

Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun sake kai wani mummanan farmaki a kananan hukumomin Ijumu da Mopa Amuro dake mazabar Kogi ta yamma na jihar Kogi, inda Sanata Dino Melaye ke wakilta a majalisar dattawa.

Jaridar The Cables ta ruwaito yan bindigar sun hallaka akalla mutane hudu, kamar yadda dan majalsar wakilai dake wakiltar kananan hukumomin biyu, Tajudeen Yusuf ya tabbatar cikin wata sanarwa da ya fitar.

KU KARANTA: Abin kunya: Kwamishinan jihar Borno ya bayyana dalilinsa na raba ma matasa kayan shushaina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan majalisa Yusuf yana cewa: “Da misalin karfe 4:30 na daren Litinin 14 ga watan Mayu wasu yan bindiga da yawansu ya kai mutum 50 sanye da kakin Soja suka kai hari a garin Iluagba, inda suka banka ma gonakai da gidaje wuta, tare da kashe mutane hudu.”

Tajudeen Yusuf ya cigaba da fadin cewa baya da kashe kashe da kone konen da suka yi, yan bindigan sun kwashe kayayyakin abinci da manoman kabilar Tibi suka tara.

A wani hari da aka sake kaiwa a ranar Talata 15 ga wata, dan majalisar yace makiyaya sun tare wanu mutane biyu da tsakar rana yayin da suke dawowa daga gona akan hanyar Obaiana zuwa Kabba, inda suka kashe guda, dayan kuma ya tsere da rauni a jikinsa,

Daga karshe Yusuf ya bayyana halin tsoro da fargaba da al’ummar yankinsa ke ciki, don haka ya nemi hukumomin tsaro da su kawo dauki, kafin maharan su karar masa da jama’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel