Sojoji sun halaka yan ta'adda 11 kuma sun ceto mata da yara 49 a jihar Borno

Sojoji sun halaka yan ta'adda 11 kuma sun ceto mata da yara 49 a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya a ranar Laraba da sanar da cewa sojojin sun kashe yan ta'adda 11 kuma sun ceto mutane 49 da 'yan ta'addan ke garkuwa da su yayin artabu da sojojin sukayi da yan ta'addan a yankin kudancin tafkin Chadi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar Lafiya Dole, Col. Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a garin Maiduguri.

Ya ce an kashe wasu 'yan ta'addan ne a yankin tafkin Chadi inda wasu daga cikinsu kuma an kashe su ne a wasu kauyuka da ke arewacin Borno a ranar Talata.

Sojoji sun halaka yan ta'adda 11 kuma sun ceto mata da yara 49 a jihar Borno

Sojoji sun halaka yan ta'adda 11 kuma sun ceto mata da yara 49 a jihar Borno

"Dakarun sojojin sun ci galaba a kan 'yan ta'addan ne a mafakarsu bayan sunyi musayar wuta, hakan ya yi sanadiyar mutuwar yan ta'adda 11 a kauyen Gomaran da ke kudancin tafkin Chadi," inji shi.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Ganduje ke min bita da kulli - Bibi Faruk

Ya cigaba da cewa dakarun sojin kuma sunyi kwantar bauna inda suka halaka wasu yan ta'adda 4 da ke hanyar su ta tsere wa daga kudancin jihar Borno.

Nwachukwu ya kuma kara da cewa dakarun sojin sun sake wata arangama da wasu 'yan ta'addan da ke hanyar su ta guduwa daga garuruwan Firgi da Moula da ke garin Bama na gundumar Dikwa.

Sojojin sun kwato kayayaki da dama wanda suka hada da karamar bindigar hannu, baushe guda daya da kuma bindiga kirar gida Najeriya.

Sauran kayan da suka gano sun hada da babura guda 4, kayayakin gyaran babur, a daidaita sahu guda , injinan samar da ruwa guda 6 da kuma janareta guda 2.

Sojin kuma sunyi nasarar ceto maza guda hudu, mata 33 da kuma yara 16 daga sansanin yan ta'addan da suka kai samamen. A halin yanzu an mika mutanen ga masana don yi musu tambayoyi kafin mika su ga sansanin yan gudun hijira kamar yadda Nwachukwu ya sanar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel