'Yan sanda sun kama matsafa 12 da laifin kisan 'ban mamaki' a jihar Bauchi

'Yan sanda sun kama matsafa 12 da laifin kisan 'ban mamaki' a jihar Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa ta gabas sun sanar da samun nasarar cafke akalla mutane 12 da suke zargi da hannu cikin kashe-kashen ban mamaki da ake yi a jihar.

Kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna DSP Kamal Datti Abubakar ya shaidawa manema labarai, garin na Bauchi a wasu unguwannin da suka hada da Fadaman Mada da Gida Dubu suna fama ne da kisan mutane a wani yanani mai ban mamaki.

'Yan sanda sun kama matsafa 12 da laifin kisan 'ban mamaki' a jihar Bauchi

'Yan sanda sun kama matsafa 12 da laifin kisan 'ban mamaki' a jihar Bauchi

KU KARANTA: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus

Legit.ng ta samu cewa DSP Kamal Datti Abubakar ya ce biyo bayan korafe korafen da suka samu daga jama'a shine sai rundunar ta soma bincike wanda hakan ya sa har suka yi wannan kamen.

A wani labarin kuma, Hukumar nan mallakin gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta kama dan majalisar dattijai dake wakiltar al'ummar yankin jihar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas mai suna Sanata Bassey Akpan.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta EFCC ta kama Sanata Bassey Akpan ne bisa zargin karbar cin hancin motocin alfarma da suka kai darajar Naira miliyan 303 daga hannun wani hamshakin mai kudi Babajide Omokore da yanzu haka yake fuskantar shari'a.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel