Fadar Shugaban Kasar ta yi karin haske kan Bidiyon da ya bayyana Sufeto Janar na 'Yan sanda na Kakarin Magana a jihar Kano

Fadar Shugaban Kasar ta yi karin haske kan Bidiyon da ya bayyana Sufeto Janar na 'Yan sanda na Kakarin Magana a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, fadar shugaban kasa ta yi martani gami da karin haske dangane da yaduwar wani Bidiyo dake bayyana sufeto Janar na 'Yan sanda, Ibrahim Idris, da yake kakarin magana yayin gabatar da jawabai a jihar Kano.

Wannan bidiyo dai ya bayyana Shugaban na 'yan sanda na kakari wajen gabatar da jawaban sa yayin kai ziyara jihar Kano a ranar Litinin da ta gabata domin kaddamar da wata cibiyar leken asiri a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya sanya shugaban na 'yan sanda ya bayar da hakuri ga masu sauraron sa.

Abike Dabiri

Abike Dabiri

Sai dai tuni wannan bidiyo ya bazu musamman a yanar gizo inda ma'abota dandalan sada zumunta ke ta tofa albarkacin bakin su tare da sharhi akan lamarin da har wasu ke ganin ya kunyata hukumar 'yan sanda ta kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a Kasashen Afirka ta Yamma

A yayin mayar da martani, babbar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin jama'a da kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa akwai shaci fadi da doriyar kage cikin wannan bidiyo.

Legit.ng ta fahimci cewa, hadimar ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta na twitter, inda take cewa tabbas shugaban na 'Yan sanda ya yi kure sau guda amma wasu 'yan adawa sun yi amfani da fasahar zamani da take nuna tamkar ya yi mai-mai a kuskuren nasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel