Wata-sabuwa: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus daga mukamin sa

Wata-sabuwa: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus daga mukamin sa

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a daren ranar Talatar da ta gabata ya yi barazanar yin murabus daga mukamin sa madamar ya ga cewa ana so a ribace shi ya bar turbar addinin sa na kiristanci.

Mataimakin shugaban kasar yayi wannan barzanar ne yayin da yake ansa tambaya daga wasu mahalarta taron da ya gudanar a gidan gwamnatin jihar lokacin ziyarar da ya kai domin ganewa idanun sa halin al'ummar jihar suke ciki.

Wata-sabuwa: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus daga mukamin sa

Wata-sabuwa: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus daga mukamin sa

KU KARANTA: Dan shekara 19 yayi wa 'yar shekara 13 ciki a Legas

Legit.ng a jawabin nasa, mataimakin shugaban kasar ya jaddadawa mahalarta taron da da yawan su malaman addinin kirista be cewa ba zai taba yadda wani abu ya taba addinin sa ba.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta fadawa mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo cewar ya fa bi a hankali domin siyasa na neman ta lalata masa imanin sa.

Jam'iyyar ta PDP wadda tayi magana a ta bakin mataimakin mai magana da yawun ta Mista Emmanuel Agbo a garin Abuja, ta kuma bayyana zuwan mataimakin shugaban kasar jihar Benue a matsayin tsantsar siyasa kawai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel