Siyasa na neman lalata maka imanin ka - Jam'iyyar PDP zuwa ga Osinbajo

Siyasa na neman lalata maka imanin ka - Jam'iyyar PDP zuwa ga Osinbajo

Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta fadawa mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo cewar ya fa bi a hankali domin siyasa na neman ta lalata masa imanin sa.

Jam'iyyar ta PDP wadda tayi magana a ta bakin mataimakin mai magana da yawun ta Mista Emmanuel Agbo a garin Abuja, ta kuma bayyana zuwan mataimakin shugaban kasar jihar Benue a matsayin tsantsar siyasa kawai.

Siyasa na neman lalata maka imanin ka - Jam'iyyar PDP zuwa ga Osinbajo

Siyasa na neman lalata maka imanin ka - Jam'iyyar PDP zuwa ga Osinbajo

KU KARANTA: Budurwa ta burma wa malamin addini fasassar kwalba

Legit.ng ta samu cewa Mista Emmanuel Agbo ya kara da cewa dole ne ya zama abun mamaki ga kowa yadda shi mataimakin shugaban kasar bai je jihar ba lokacin da ake ta kashe-kashen sai yanzu da yaga zaben 2019 ya kusa zuwa.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a daren ranar Talatar da ta gabata ya yi barazanar yin murabus daga mukamin sa madamar ya ga cewa ana so a ribace shi ya bar turbar addinin sa na kiristanci.

Mataimakin shugaban kasar yayi wannan barzanar ne yayin da yake ansa tambaya daga wasu mahalarta taron da ya gudanar a gidan gwamnatin jihar lokacin ziyarar da ya kai domin ganewa idanun sa halin al'ummar jihar suke ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel