Farashin gangar danyen mai ya kai $80 bayan kusan shekaru 4

Farashin gangar danyen mai ya kai $80 bayan kusan shekaru 4

Farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya yanzu haka ta kai kusa dalar Amurka 80 a karon farko tun a shekarar 2014, kusan shekaru 4 kenan biyo bayan takaddamar da ke cigaba da wanzuwa tsakanin kasar Amurka da Iran.

Mun samu daga majiyar mu ta Brent crude dai ta bayyana cewa farashin kuma zai iya ya cigaba da hawa idan dai har rashin jituwa a tsakanin kasashen biyu masu arzikin man ta cigaba da wanzuwa.

Farashin gangar danyen mai ya kai $80 bayan kusan shekaru 4

Farashin gangar danyen mai ya kai $80 bayan kusan shekaru 4

KU KARANTA: Jami'an kwastam sun kama motocin alfarma 30

Legit.ng dai ta samu cewa tashin farashin man a kasuwar duniya na nufin samun karin kudaden shiga a wurin gwamnatin tarayya yayin da kuma a hannu guda kudin da take biya a wajen tallafin mai zai karu shima.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Borno dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Kashim Shettima a ranar Alhamis mun samu cewa ya aike da takardar sammaci tare da karin bayani zuwa ga kwamishin harkokin ilimi mai zurfi a jihar.

Gwamnan ya dai aike ta takardar ne zuwa ga kwamishinan kuma dan takarar zama dan majalisar tarayya a jihar Usman Jaha (Babawo) bisa wani abun kunya da ya ja wa jihar na rabawa al'ummar mazabar sa kayan wankin takalma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel