Shehu Sani yayi magana bayan Shugaban APC yayi barazanar ficewa daga Jam’iyya

Shehu Sani yayi magana bayan Shugaban APC yayi barazanar ficewa daga Jam’iyya

- Segun Oni yace ana neman matsa masa ya bar Jam’iyyar APC

- Kwanaki E. Oni ya rika kokarin hada-kan APC a Jihar Kaduna

- Shehu Sani wanda ke rikici da Gwamnan Kaduna yayi tanbihi

Kwanakin baya kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kudancin Najeriya Injiniya Segun Oni ya bayyana cewa idan aka yi sake fa zai tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar saboda banbancin da ake nuna masu a tafiyar.

Shehu Sani yayi magana bayan Shugaban APC yayi barazanar ficewa daga Jam’iyya

Shehu Sani ya tofa albarkacin bakin sa game da kukan Oni

Tsohon Gwamnan na Jihar Ekiti Segun Oni ya koka da abin da yake faruwa a Jam’iyyar APC. Segun Oni yayi jawabi ga Magoya bayan sa bayan ya sha kasa a zaben fitar da gwani na takarar Gwamnan na Ekiti a karkashin APC.

A baya Segun Oni aka sa ya sasanta rikicin da ya barke a Jam’iyyar a Kaduna tsakanin Gwamnan da ‘Yan Majalisar Dattawa. Sai dai jim kadan bayan kokarin kawo gyara a APC sai aka ji jigon Jam’iyyar yana shirin tserewa.

KU KURANTA: Shugaba Buhari ya halarci tafsiri na Watan Ramadan

Sanata Shehu Sani wanda ba su ga maciji da Gwamnan na Kaduna Nasir El-Rufai yace wannan karo an tare mai tare bayan da ya ji Oni yana kukan rashin adalci a Jam’iyyar. Har yanzu dai wutan rikicin APC a Jihar ba ta mutu ba.

‘Dan takarar Gwamnan yace ana neman maida magoya bayan sa saniyar ware a APC da zarar Dr. Kayode Fayemi ya samu darewa kujerar Gwamnan Jihar. Ministan Buharin ne dai ya doke Oni wajen zaben fitar da gwani na APC a Ekiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel