Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana masu haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana masu haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a ranar Alhamis din da ta gabata ta jajirce akan cewa gwamnonin jihohi ke haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma a fadin Kasar nan.

Babban Sakataren kungiyar na kasa, Baba Ngelezarma, shine ya bayyana hakan yayin taron ganawa da al'umma da gwamnatin tarayya ta shirya gudanarwa a babban birnin tarayya na Abuja.

Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana masu haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana masu haddasa rikici tsakanin Makiyaya da Manoma

Ngelezarma ya kuma bayyana cewa, kungiyar ta Miyetti Allah ba ta juya ba ga samar da yankunan kiwo ba hakazalika ba ta dauke kafar ta ba wajen kiwatar dabbobi, inda ya nemi gwamnatin akan ta samar da yankunan kiwo da zasu kasance abin sha'awa ga makiyaya.

KARANTA KUMA: Yahaya Bello ya shawarci Shugaba Buhari akan yadda ya dace a sarrafa kudaden da aka Kwato daga hannun Barayin Gwamnati

Babban sakataren ya kuma tsarkake gwamnatin tarayya daga cikin alhakin haddasa rikicin makiyaya da manoma a kasar nan, inda yake cewa hakki ne na gwamnatocin jihohi da rataya a wuyansu.

Ya kara da cewa, hakki ne akan gwamnatocin kowace jiha ta samar da tsaro da kuma ilimi domin kuwa suke da alhakina yankunan jihohin su wajen kyautata zamantakewar al'ummomin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel