Buhari ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a Kasashen Afirka ta Yamma

Buhari ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a Kasashen Afirka ta Yamma

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashi na cewar gwamnatin sa za ta ci gaba da goyon baya tare da bayar da hadin kai ga kungiyar kasashen Afirka ta Yamma domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban ya bayyana cewa, wannan hadin kai ya zamto wajibi ne sakamakon miyagun laifuka da ke ta afkuwa a iyakokin kasashen da hakan ke janyo barazana ga al'umma da kuma gwamnatocin kasashe na yankin.

Buhari ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a Kasashen Afirka ta Yamma

Buhari ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a Kasashen Afirka ta Yamma

A wani rahoto da sanadin kakakin shugaban kasar Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya yi wannan sanarwa ne yayin tarba da karrama jakadan kasar Guinea Bissau, Mista Henrique Da Silva a fadar sa dake babban birni na tarayya.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar

Shugaba Buhari ya yi wannan sanarwa ne da cewar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma tana iyaka bakin kokarin ta wanda a yanzu Najeriya tana bayar da gudunmuwar ta wajen wanzar da kwanciyar hankali a kasar Guinea Bissau.

A yayin haka kuma, shugaba Buhari ya karrama sabon jakadan kasar Thailand zuwa Najeriya, Mista Wattana Kunwongse, inda ya bayyana cewa akwai kyakkyawar danganta a tsakanin kasashen biyu ta manufar habaka tattalin arziki musamman a fannin harkokin noma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel