Da dumin-dumi: Harin kunar bakin wake a masallaci ya hallaka mutane hudu a Maiduguri

Da dumin-dumi: Harin kunar bakin wake a masallaci ya hallaka mutane hudu a Maiduguri

A kalla mutane hudu ne suka mutu a yau, Alhamis, bayan wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani masallaci dake sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Dan kunar bakin wake ya saje ne cikin masu ibada tare da tashin bam din dake jikin sa a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Dikwa mai nisan kilomita 90 a gabashin Maiduguri.

‘Da sanyin safiyar yau ne wani dan kunar bakin wake ya kasha mutane hudu tare da raunata wasu 15 bayan ya tashi bam din dake jikin sa a wani budadden masallaci dake wani sansani a Dikwa,” a cewar wani jami’I, Babakura Kolo, dake aiki a wurin.

Da dumin-dumi: Harin kunar bakin wake a masallaci ya hallaka mutane hudu a Maiduguri

Da dumin-dumi: Harin kunar bakin wake a masallaci ya hallaka mutane hudu a Maiduguri

Ya kara da cewar, dan harin kunar bakin waken ya kai harin ne da misalign karfe 5:17 na asuba. An garzaya da mutanen da suka samu raunuka asibiti domin basu kulawa.

Akwai ‘yan gudun hijira fiye da 70,000 dake zaune a sansani daban-daban a garin Dikwa sakamakon rasa muhallin su a yakin da Boko Haram.

DUBA WANNAN: Dan sanda ya kashe kan sa saboda an yi masa canjin wurin aiki

A wani labarin na Legit.ng kun karanta cewar, 'yan sanda a kasar Sudan sun yiwa wata mata bulala 75 bayan kotu ta same ta da laifin yin aure ba tare da amincewar mahaifinta ba.

Matar, 'yar asalin yankin Dafur mai fama da yaki, an yi mata bulalar ne a ofishin 'yan sanda na Omdurman dake Khartoum, bayan ta shafe watanni shida a gidan yari.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan wata kotun Sudan din ta yankewa wata matashiya hukuncin kisa saboda ta kashe mijinta bayan ya tilasta mata kwanciya da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel