Yahaya Bello ya shawarci Shugaba Buhari akan yadda ya dace a sarrafa kudaden da aka Kwato daga hannun Barayin Gwamnati

Yahaya Bello ya shawarci Shugaba Buhari akan yadda ya dace a sarrafa kudaden da aka Kwato daga hannun Barayin Gwamnati

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan hanyoyin da suka dace a kasar nan wajen sarrafa kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

Gwamna Bello ya shawarci shugaba Buhari akan yin amfani da wannan kudade a harkokin noma, sana'o'in hannu da kuma kananan masana'atu da ake samu riba mai tsoka matukar an jajirce gami da hakuri yayin nema.

Yahaya Bello ya shawarci Shugaba Buhari akan yadda ya dace a sarrafa kudaden da aka Kwato daga hannun Barayin Gwamnati

Yahaya Bello ya shawarci Shugaba Buhari akan yadda ya dace a sarrafa kudaden da aka Kwato daga hannun Barayin Gwamnati

Lamba dayan na al'ummar jihar Kogi ya bayyana cewa, ire-iren wannan kananan sana'o'i masana'an tu sune kan gaba ta fuskar nakasu da barazanar cin hanci da rashawa ta fi muzantawa.

KARANTA KUMA: Wani Matashi 'Dan Shekara 25 ya Kashe Budurwa sakamakon rashin amincewa da Soyayyar sa

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan ya yi wannan hangen nesan ne yayin kaddamar da shirin noman damina a birnin Lokoja, inda ya ce Najeriya za ta ci babbar nasara muddin aka sanya hannun jari mai tsoka cikin harkokin noma.

A yayin haka kuma, gwamna ya taya shugaba Buhari murna dangane da mashahuranci daya samu a idon duniya a sakamakon akidar sa ta yakar cin hanci da rashawa wajen kwato kudaden da aka handame na kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel