Kotu ta daga shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ya gani

Kotu ta daga shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ya gani

- Babbar kotun birnin tarayya a ranar Alhamis ta daga sauraron shari’ar Sanata Dino Melaye na jihar Kogi, dagawa ta har sa baba yagaisakamakon matsalar rashin lafiyarsa

- Hukumar ‘Yan Sanda tana karar Sanata Melaye a birnin tarayya da kuma garin Lokoja, inda a birnin tarayya suke zarginsa da yunkurin kashe kansa da kuma bata kayan gwamnati

- A garin Lokoja kuma ‘Yan Sandan na tuhumarsa da laifin yiwa hukumar karya da kuma bawa ‘yan ta’adda makamai

Babbar kotun birnin tarayya a ranar Alhamis ta daga sauraron shari’ar Sanata Dino Melaye na jihar Kogi, dagawa ta har abada sakamakon matsalar rashin lafiyarsa.

Hukumar ‘Yan Sanda tana karar Sanata Melaye a birnin tarayya da kuma garin Lokoja, inda a birnin tarayya suke zarginsa da yunkurin kashe kansa da kuma bata kayan gwamnati, wanda sanadiyar haka aka kwantar da shi a asibiti.

Kotu ta daga shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ya gani

Kotu ta daga shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ya gani

A garin Lokoja kuma ‘Yan Sandan na tuhumarsa da laifin yiwa hukumar karya da kuma bawa ‘yan ta’adda makamai.

KU KARANTA KUMA: Kasar Najeriya zata hadu da fushin Allah idan gwamnati bata saki El-Zakzaky ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Alkalin na birnin tarayya Olasunbo Goodluck, ya bukaci Lauyan wanda ake kara, Rickey Tarfa, ya bayar da kwakwaran bayani game da rashin bayyanar Melaye a gaban kotun aranar Laraba, inda ya gabatar da takardunsa asibiti a gaban kotun.

Sakamakon haka kotun ta gamsu da cewa Mr. Melaye, yana kwance a asibiti bangaren wadanda ake bawa kula ta musamman, wanda dalilin hakan ne Alkalin kotun Goodluck ya daga shari’ar dagawa ta har abada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel