Akwai almundahana cikin kudin tallafin man fetur – Gwamnoni suna zargin NNPC

Akwai almundahana cikin kudin tallafin man fetur – Gwamnoni suna zargin NNPC

Kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, suna zargin babban kamfanin man feturin Najeriya da ninka yawan man da Najeriya ke sha a kowani ranan daga lita miliyan 30 zuwa miliyan 60.

Kana gwamnonin sun bukaci bincike mai zurfi cikin kudin tallafin man da aka biya daga shekarar 2015 ila yau.

Wata tawagar kungiyar wacce shugaban, AbdulAziz Yari ya jagoranta sun mika bukatarsu ne a wani ganawa da sukayi da mataimakin shugaban kasa, Faresa Yemi Osinbajo, a fadar shugaban kasa.

Akwai almundahana cikin kudin tallafin man fetur – Gwamnoni suna zargin NNPC

Akwai almundahana cikin kudin tallafin man fetur – Gwamnoni suna zargin NNPC

Gwamnonin da suka halarci taron sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki; gwamanan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; da gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson.

KU KARANTA: EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati

Daga cikin ministocin da suka halarta sune ministan kudi, Mrs Kemi Adeosun da ministan kasafin kudi, Sanata Udoma Udoma.

Gwamnonin sun umarci NNPC da fayyace kudaden da ke shigowa aljihunsu kafin turawa asusun gwamnati domin komai ya fito fili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel