Sanatoci sun kuma yin tir da zubar da jinin da ake yi a Najeriya

Sanatoci sun kuma yin tir da zubar da jinin da ake yi a Najeriya

- Majalisar Dattawa tayi Allah-wadai da kashe-kashen da ake yi

- Har yanzu ana kashe Bayin Allah babu gaira-babu dalili a Kasar

- Bukola Saraki yace za su gayyaci Jami’an tsaro gaban Majalisa

Majalisar Dattawa ta koka da yadda ake asarar rayuka a Najeriya inda wasu Sanatoci su kayi kira a kawo karshen lamarin. Sanatoci da dama sun yi magana a Majalisar Kasar inda su kace ya kamata Jami’an tsaro su dage.

Sanatoci sun kuma yin tir da zubar da jinin da ake yi a Najeriya

Jami’an tsaro na cigaba da kokarin kare rayukan jama’a

Sanatocin Kasar sun kuma yin tir da zubar da jinin da ake yi a kasar ne a zaman da su kayi a makon nan. Sanata Shehu mai wakiltar Kaduna ta tsakiya karkashin APC ya nemi ayi wani abu game da barnar da ake yi a Birnin Gwari.

Sanata Shehu Sani yace a kusan kullum cikin kashe mutane ake yi a garin Birnin Gwari har ta kai Manoma da sauran Jama’a na tserewa daga Garin. Sanatan na APC ya nemi a baza Sojoji domin su yi maganin ta’asar kurum a huta.

KU KARANTA: 'Dan Sanda ya harbe wani Soja har lahira a Ribas

Shi ma dai Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya koka da lamarin da kan sa. Saraki yayi magana game da mutane 87 da aka ce an sace a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda yace dole Jami’an tsaro su bayyana gaban su.

Kuma kun ji cewa sai jiya ne Allah yayi Majalisun Tarayyar Kasar su ka amince da kasafin kudin 2018 wanda yake hannun su tun farkon Nuwamban bara. Ana sa rai za a kashe Biliyan 50 kan harkar tsaro a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel