Tirkashi: Kotun Najeriya ta yankewa wani mutum daurin shekaru 2,670 a gidan yari, karanta laifin day a aikata

Tirkashi: Kotun Najeriya ta yankewa wani mutum daurin shekaru 2,670 a gidan yari, karanta laifin day a aikata

- Wata kotun majistare dake zaman ta a Ebute-Meta dake Legas ta yankewa wani dillali, Alhaji Ayobami Oseni, hukuncin daurin shekaru 2,670 a gidan yari

- Alkalin kotun, O. O. Olatunji ya yankewa Oseni wannan hukunci ne bayan ya amsa cewar ya aikata laifukan dake cikin dukkan tuhuma 267 da ake yi masa

- Oseni zai yi zaman gidan yarin ne a lokaci guda, ma’ana zai yi zaman gidan yarin ne na tsawon shekaru goma kacal

Wata kotun majistare dake zaman ta a Ebute-Meta dake Legas ta yankewa wani dillali, Alhaji Ayobami Oseni, hukuncin daurin shekaru 2,670 a gidan yari saboda damfarar masu neman 133 kudi, miliyan N25m.

Tirkashi: Kotun Najeriya ta yankewa wani mutum daurin shekaru 2,670 a gidan yari, karanta laifin day a aikata

Alhaji Ayobami Oseni

Alkalin kotun, O. O. Olatunji ya yankewa Oseni wannan hukunci ne bayan ya amsa cewar ya aikata laifukan dake cikin dukkan tuhuma 267 da ake yi masa, da suka hada da zamba cikin aminci, yaudara, da kuma karya.

DUBA WANNAN: Kotu tayi umarnin yiwa wata amarya bulala 75 bayan ta gama zaman gidan yari na wata 6 saboda ta aurin mutumin da mahaifinta baya so

Olatunji ya bayyana cewar laifukan Oseni sun ci karo da sashe 285, 312 da 409 na kundin aikata laifuka na jihar Legas, a saboda haka ya yankewa Oseni hukuncin daurin shekaru 10 a kan kowacce tuhuma daga cikin 267 da ake yi masa.

Oseni zai yi zaman gidan yarin ne a lokaci guda, ma’ana zai yi zaman gidan yarin ne na tsawon shekaru goma kacal. Zai fara zaman gidan yarin ne daga ranar 26 ga watan Afrilu bayan kotun ta ki amincewa da rokon bayar das hi beli. Saidai wasu ‘yan Najeriya masana shari’a sun ce idan aka cire shekara guda da Oseni ya yi a gidan yarin kafin yanke masa hukunci, zai yi shekaru 9 ne a cikin hukuncin zaman shekaru 10 da kotun ta yanke masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel