Yan ta’adda sun kaiwa ayarin motocin kakakin majalisar jihar Katsina hari

Yan ta’adda sun kaiwa ayarin motocin kakakin majalisar jihar Katsina hari

- Wasu mutane biyu sunyiwa gungun ‘yan ta’adda jagora wurin harin ayarin motocin kakakin majalisa, Abubakar Kusada, an gurfanar dasu a gaban kotun jihar Katsina

- Wadanda ake zargin Shamsu Rabiu 25, da kuma Anas Abdullahi 22, wadanda duk mazauna garin Gidan Mutum Daya ne, suna fuskantar shari’a bisa laifin ta’addanci da kuma hana zaman lafiya

- ‘Yan Sanda sun bayyanawa kotun cewa lamarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Mayu, 2018, lokacin da shugaban majalisar ke dawowa daga tafiyar da yayi don gudanar da wani aiki

Wasu mutane biyu sunyiwa gungun ‘yan ta’adda jagora wurin harar jerin motocin kakakin majalisa, Abubakar Kusada, an gurfanar dasu a gaban kotun jihar Katsina.

Wadanda ake zargin Shamsu Rabiu 25, da kuma Anas Abdullahi 22, wadanda duk mazauna garin Gidan Mutum Daya ne, suna fuskantar shari’a bisa laifin ta’addanci da kuma hana zaman lafiya.

Laifin wanda hukumar ‘Yan Sanda tace ya sabawa sashe na 97, 327, 113, 124 da kuma 247, na dokar jihar Katsina.

Yan ta’adda sun kaiwa ayarin motocin kakakin majalisar jihar Katsina hari

Yan ta’adda sun kaiwa ayarin motocin kakakin majalisar jihar Katsina hari

‘Yan Sanda sun bayyanawa kotun cewa lamarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Mayu, 2018, lokacin da shugaban majalisar ke dawowa daga tafiyar da yayi don gudanar da wani aiki. Inda suka tare hanyar gidan mutum daya suna kona tsintsinya.

KU KARANTA KUMA: Kasar Najeriya zata hadu da fushin Allah idan gwamnati bata saki El-Zakzaky ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Bayan rahoto da Alkasim ya kai ofishin ‘Yan Sanda dake kusada, haka yasa akayi nasarar kama Rabiu da Abdullahi, sai kuma wani Abdulgafar Aminu da ya gudu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel