Hankula sun tashi a Fatakwal bayan wani 'dan sanda ya bindige soja har lahira

Hankula sun tashi a Fatakwal bayan wani 'dan sanda ya bindige soja har lahira

Mutanen unguwar Ada Goerge da ke garin Fatakwal na jihar Ribas sun tashi cikin tashin hankali bayan wani jami'in dan sanda ya bindige wani soja har lahira.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, jami'in dan sandan bai san cewa mutumin soja bane kuma ya dirka masa harsashi har sau biyu wanda hakan tayi sanadiyyar rasuwar sa.

kwamishina yan sanda na jihar Ribas, Zaki Ahmed ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba gaskiya bane cewa sojojin suna rigima da jami'an yan sanda.

Hankula sun tashi a Fatakwal bayan wani 'dan sanda ya bindige soja har lahira

Hankula sun tashi a Fatakwal bayan wani 'dan sanda ya bindige soja har lahira

KU KARANTA: 'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

Kisan da akayi wa sojan ya janyo tashin hankali da cinkoso a titunan babban birnin jihar ta ribas inda aka rufe wasu titunan wanda hakan ya jefa masu ababen hawa cikin halin tsaka mai wuya.

Mazauna garin na Fatakwal da dama sunyi amfani da shafukkan sada zumnta na zamani inda suke bayyana irin halin kakani-kayi da garin ta shiga sakamakon wannan lamarin.

Mutane dai suna ta guje-guje inda suke neman wuraren da zasu buya saboda gudun abinda ka iya biyo baya daga jami'an sojojin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel