Yadda shugaban NEMA, Maihaja ya ki amincewa da shirin bayar da tallafin shinkafa ga ‘Yan gudun hijira amma ya siya ton 5000 da kudaden al’umma

Yadda shugaban NEMA, Maihaja ya ki amincewa da shirin bayar da tallafin shinkafa ga ‘Yan gudun hijira amma ya siya ton 5000 da kudaden al’umma

- Majalisa ta kalubalanci hukumar bayar da agajin gaggawa akan kin amincewa da shirin bayar da taimakon abinci WFP, ga ‘yan gudun hijira amma kuma suka dauki kudin jama’a suka siyo tan 5000 na shinkafa don bawa ‘yan gudun hijirar

- Yan majalisa sun nuna bacin ransu sakamakon Mr Kayode da ya kasa amsa masu tambayar da akayi masa tare da Hon Mohammed Nur Sherrif wadanda ke wakiltar inda matsalar tafi shafa kamarsu Bama/Ngala/Kalabalge a jihar Borno

- Gwamnatocin 5 cikin jihohin 6 wadanda ya kamata su samu wannan tallafi na shinkafar, sun bayyana cewa basu karbi tallafin komai ba daga wannan shiri

Majalisa ta kalubalanci kungiyar bayar da tallafin abinci akan kin amincewa da kungiyar bayar da taimakon abinci WFP, akan bawa ‘yan gudun hijira tallafin abinci, amma kuma sun dauki kudin jama’a sun siyo tan 5000 na shinkafa don bawa ‘yan gudun hijirar.

Kayode Fagbemi, Daraktan NEMA mai rukon kwarya, wanda ya wakilci Darakta Janar Mustapha Maihaja, na hukumar, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu umurnin rabar da shinkafa tan 10,000 ga ‘yan gudun hijirar sannan su bawa WFP wani sashe na rarrabar don a gaggauta rabon.

Yadda shugaban NEMA, Maihaja ya ki amincewa da shirin bayar da tallafin shinkafa ga ‘Yan gudun hijira amma ya siya ton 5000 da kudaden al’umma

Yadda shugaban NEMA, Maihaja ya ki amincewa da shirin bayar da tallafin shinkafa ga ‘Yan gudun hijira amma ya siya ton 5000 da kudaden al’umma

KU KARANTA KUMA: Kasar Najeriya zata hadu da fushin Allah idan gwamnati bata saki El-Zakzaky ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Yan majalisa sun nuna bacin ransu sakamakon Mista Kayode da ya kasa amsa masu tambayar da akayi masa tare da Hon Mohammed Nur Sherrif wadanda ke wakiltar inda matsalar tafi shafa kamarsu, Bama / Ngala / Kalabalge a jihar Borno, sakamakon kasa bayyana masu da yayi na inda aka kai shinkafar tinda sansanin ‘yan gudun hijirar sunce basu karba ba.

Gwamnatocin 5 cikin jihohin 6 wadanda ya kamata su samu wannan tallafin shinkafar, sun bayyana cewa basu karbi tallafin komai ba daga wannan shirin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel