Abinda Buhari ya fadawa Tinubu, Osinbajo, da Oyegun a kan zaben jihar Ekiti

Abinda Buhari ya fadawa Tinubu, Osinbajo, da Oyegun a kan zaben jihar Ekiti

Shugaba Muhammadu Buhari ya kallubalanci shuwagabanin jam'iyyar APC na yankin kudu maso yamma da su zage damtse dan ganin jihar Ekiti da dawo karkashin mulkin gwamnatin jam'iyyar APC bayan zaben da za'a gudanar cikin yan kwanakin nan.

Shugaban kasan ya yi wannnan kira ne a yayin wata liyafa da ya shirya wa shugabanin a jihar Laraba a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Zaben jihar Ekiti: Abinda shugaba Buhari ya fadawa jiga-jigan APC na kudu maso yamma

Zaben jihar Ekiti: Abinda shugaba Buhari ya fadawa jiga-jigan APC na kudu maso yamma

Cikin wadanda suka hallarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bola Tinubu da Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun.

KU KARANTA: 'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

Shugaban kasan ya kallubalance su da tabbatar cewa dan takarar jam'iyyar APC, Kayode Fayemi ya lashe zaben da za'a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli na shekarar 2018.

"A halin yanzu da muke tunkarar zaben 2019, dawo da jihar Ekiti karkashin mulkin jam'iyyar masu son cigaba a zaben 14 ga watan Yuli yana da matukar muhimmanci don hakan wata alama ce kan yadda babban zaben za ta kasance," inji shugaba Buhari.

Shugaban kasan kuma ya jadada cewa ba zaiyi katsalandan cikin harkokin cikin gida na jihohi ba kuma ya yabawa ministan ma'adinai, Kayode Fayemi kan yadda ya nuna goyon baya ga takwarorinsa da suka fadi zabe a ranar Asabar da ta gabata.

Ya kuma yi kira ga dukkan mambobi da magoya bayan jam'iyyar APC su dauki zaben na ranar 14 ga watan Yuli a matsayin wata aiki da za suyi don ceto jihar Ekiti da kuma kawo cigaba a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel