‘Yan bindiga sun tarwatsa taron jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba

‘Yan bindiga sun tarwatsa taron jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba

a jiya ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka dira wurin taron jam’iyyar APC a karamar hukumar Yakurr dake jihar Kuros Riba tare da tarwatsa mutane ta hanyar yin harbin iska.

Wani shaidar gani da ido, da ya ce sunan sa Ibor, ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun tarwatsa jama’a tare da fadin cewar ba za a yi taron ba tunda minista bai zo ba.

A tilas shugabancin jam’iyyar APC tare da masu ruwa da tsakai na jam’iyyar suka daga taron har sai baba-ta-gani.

‘Yan bindiga sun tarwatsa taron jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba

Uguru Usani

Da yake Magana da manema labarai, Shugaban kwamitin taron jam’iyyar APC a karamar hukumar Yakurr, Mista Owan Kenneth, ya tabbatar da samun barkewar rikici yayin gudanar da taron. Ya bayyana cewar lamarin ya kara lalacewa ne bayan wasu ‘yan bindiga sun dira tare da yin harbin iska a wurin.

Kenneth ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda dake makwabtaka da wurin taron, inda suka wulla duwatsu tare da lalata kokfofi, tagogi da wata mota guda a ofishin ‘yan sandan.

DUBA WANNAN: Buhari ya fi karfin Kwankwaso a Kano - El-Rufa'i

Karamar hukumar Yakurr ce mahaifar ministan yankin Naija-Delta, Usani Uguru Usani.

Babu rahoton rasa rai ko samun rauni sakamakon harin ‘yan bindigar.

An samu hargitsi a jihohin yankin Naija-Delta tare da kasha mutum guda a jihar Delta yayin gudanar da zabukan shugabannin mazabu na jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel