El-Zakzaky: Sojoji a shirye suke dasu fuskanci ‘yan shi’a, idan har basu daina zanga-zangar tayar da rikici ba

El-Zakzaky: Sojoji a shirye suke dasu fuskanci ‘yan shi’a, idan har basu daina zanga-zangar tayar da rikici ba

- Hukumar Sojojin Najeriya tace Sojoji a shirye suke a birnin tarayya da fuskantar kungiyar ‘yan Shi’a masu cigaba da gudanar da zanga-zangar tayar da hankali a birnin tarayya akan tsare shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

- Kwamandan guards Brigade, Brigadier-Janar Umar Tama Musa, ya bayyana haka a wurin bude gasar motsa jini ta sojojin a birnin tarayya

- Kwamandan yace tabbas hakkinsu ne su bawa shugaban kasa da iyalansa kariya da kuma mutanen dake birnin tarayyar duk da cewa yanzu lamarin na hannun ‘Yan Sanda kuma suna daukar matakin da ya kamata

Hukumar Sojojin Najeriya tace Sojoji a shirye suke a birnin tarayya da fuskantar kungiyar ‘yan Shi’a masu cigaba da gudanar da zanga-zangar tayar da hankali a birnin tarayya akan tsare shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Kwamandan guards Brigade, Brigadier-Janar Umar Tama Musa, ya bayyana haka a wurin bude gasar motsa jini ta sojojin a birnin tarayya.

El-Zakzaky: Sojoji a shirye suke dasu fuskanci ‘yan shi’a, idan har basu daina zanga-zangar tayar da rikici ba

El-Zakzaky: Sojoji a shirye suke dasu fuskanci ‘yan shi’a, idan har basu daina zanga-zangar tayar da rikici ba

Kwamandan yace “tabbas hakkinmu ne mu bawa shugaban kasa da iyalansa kariya da kuma mutanen dake birnin tarayyar duk da cewa yanzu lamarin na hannun ‘Yan Sanda kuma suna daukar matakin da ya kamata."

KU KARANTA KUMA: Kotu ta dage sauraron shariar manyan ‘yan jam’iyyar PDP 5 da ake tuhumar da laifin cin hanci da rashawa

Zakzaky da matar tasa Zainab, a ranar Talata, aka dauke su daga ofishin DSS dake birnin tarayya zuwa jihar kaduna domin gurfana a gaban kotu bisa laifin da ake tuhumar su a kai na tara jama’a ba bisa ka’ida ba.

An kuma dawo dasu zuwa birnin tarayya a wannan rana da aka tafi dasu, domin a cigaba da tsaresu a karkashin kulawar hukumar DSS kamar yadda kotu ta bayar da umurni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel