Hatsaniyar Majalisa: An janyewa wani Sanata jami'an tsaro saboda ya caccaki shugaban 'yan sanda Ibrahim K. Idris

Hatsaniyar Majalisa: An janyewa wani Sanata jami'an tsaro saboda ya caccaki shugaban 'yan sanda Ibrahim K. Idris

-

Sanata Emmanuel Bwacha daga jihar Taraba ta Kudu ya bayyanawa 'yan uwansa Sanatoci yadda aka janye masa Jami'an tsaron dake kare lafiyarsa, sakamakon nuna rashin goyon baya da ya yi game da rashin amsa gayyatar da Majalisa ta yi wa babban sufeton 'yan sanda Ibrahim K Idris.

Badakalar Majalisa: An janyewa wani sanata jami'an tsaro saboda ya caccaki shugaban 'yan sanda Ibrahim K. Idris

Badakalar Majalisa: An janyewa wani sanata jami'an tsaro saboda ya caccaki shugaban 'yan sanda Ibrahim K. Idris

Mista Bwacha ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karin haske game da makarkashiyar da ake kokarin kullawa shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki.

Ya bayyana yadda jami'an tsaronsa sun kaurace masa bayan ya bukace su domin yin tafiya zuwa garin Jos.

KU KARANTA: Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ne kadai ba maciya amana ba – Inji Buhari

"Ranar alhamis na shirya domin tafiya daga Abuja zuwa Jos, muna cikin tafiya sai 'yan sandan suka sanar da ni cewa an basu umarnin cewa da su kaurace min sannan su koma caji ofis mafi kusa, abin ya bani mamaki, ni kuwa sai na kada baki nace ko dan na nuna abinda Shugaban 'Yan sanda yayi bai kyauta ba saboda rashin amsa gayyatar da Majalisa ta masa".

"Haka nan suka barni cikin halin fargaba da tsoro ni kadai, na tsaya cikin damuwa da zullumi daga bisani na yanke shawarar kyale su su tafi ba tare da sun san a ina zan sauka ba. Washegari haka na dawo Abuja ni kadai cikin kadaici da fargaba". Ini Sanatan

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel