Dan takarar shugaban kasa ya yi zargin cewa ayyuka miliyan 9 aka rasa a karkashin Buhari

Dan takarar shugaban kasa ya yi zargin cewa ayyuka miliyan 9 aka rasa a karkashin Buhari

- Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, yace kayar da shugaba Buhari a zaben 2019 abu ne mai sauki

- Moghalu wanda ke neman takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da yake kaddamar da kungiyar magoya bayansa a garin Awka

- Moghalu yace Buhari ya zubar da mutuncinsa a idon mutanen Najeriya wadanda suka tsaya masa yaci zabe a shekarar 2015

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, yace kayar da shugaba Buhari a zaben 2019 abu ne mai sauki.

Moghalu wanda ke neman takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da yake kaddamar da kungiyar magoya bayansa a garin Awka dake jihar Anambra.

Dan takarar shugaban kasa ya yi zargin cewa ayyuka miliyan 9 aka rasa a karkashin Buhari

Dan takarar shugaban kasa ya yi zargin cewa ayyuka miliyan 9 aka rasa a karkashin Buhari

Moghalu yace Buhari ya zubar da mutuncinsa a idon mutanen Najeriya wadanda suka tsaya masa yaci zabe a shekarar 2015.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso ba zai iya hana shugaba Buhari cin kano ba – Inji El-Rufa'i

Yace zaiyi amfani da rashin kokarin da Buhari yayi a mulkinsa a matsayin makamin da zaiyi amfani dashi don ya kada Buhari zabe a shekarar 2019.

Yana mai karawa da cewa tinanin da mutane keyi na cewa shugaban kasa a shekarar 2019, ya kasance dan arewa wannan rashin tinani ne kuma an kori wannan tinanin ma daga Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel