Babbar mota ta murkushe dalibar jami'a har lahira

Babbar mota ta murkushe dalibar jami'a har lahira

A jiya Laraba ne daliban jami'ar Ilimi ta Tai Solarin TASUED da ke Ijebu-Ode su kayi wata zanga-zanga saboda rasuwar wata dalibar jami'ar, Kofoworola Toibat Kuku wanda wata babban mota ta markade ta a titin Benin Ore -Lagos.

An gano cewa direban babban motar ya buge dalibar ne kuma ya tsere a yayinda ta ke kan babbur din haya (Acaba) kan hanyarta na zuwa makaranta kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Babbar mota ta murkushe dalibar jami'a har lahira

Babbar mota ta murkushe dalibar jami'a har lahira

Majiyar Legit.ng ta gano cewa daliban sun kafa shinge inda suka hana motocci wucewa kan titin Benin-Ore-Legas inda suka kona itatuwa da tayoyi a kan titin don nuna baccin ransu game da kisar gillar da akayi wa takwararsu.

KU KARANTA: 'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

Kwamandan hukumar kare haddura, (FRSC) Clement Oladele ya tabbatar da faruwar hadarin inda ya ce an gano gawar dalibar mai suna Kofoworola Toibat Kuku.

Oladele ya ce mai babur din ya tsira da ransa a hatsarin da ya faru misalin karfe 12:15 na rana inda ya kara da cewa jami'an hukumar ta FRSC sun dauke gawar dalibar zuwa dakin ajiye gawa na asibitin gwamnati da ke Ijebu-Ode.

Jami'in hulda da al'umma na hukumar Yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce kwamishinan yansanda, Ahmed Iliyasu ya bayar da umurnin aikewa da yansandan kwantar da tarzoma zuwa makarantar amma a halin yanzu babu wanda aka kama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel