Kotu ta dage sauraron shariar manyan ‘yan jam’iyyar PDP 5 da ake tuhumar da laifin cin hanci da rashawa

Kotu ta dage sauraron shariar manyan ‘yan jam’iyyar PDP 5 da ake tuhumar da laifin cin hanci da rashawa

- Babbar kotun tarayya wadda ke zama a garin Benin, ta daga sauraron karar Osagie Ize-Iyamu, Lucky Imasuen, Dan Orbih, Tony Azigbemi da kuma Efe Erimuoghae Anthony, zuwa 11 ga watan Yuni, 2018

- Ana zargin su da hada kai wurin satar kudaden gwamnatin jihar wanda ya sabawa dokar kasa

- A zaman da kotun tayi a ranar Laraba, bata samu damar tuhumar wadanda ake zargin ba sakamakon rashin bayyanar Ize- Iyamu da kuma Dan Orbih a gaban kotun

Babbar kotun tarayya wadda ke zama a garin Benin, ta daga sauraron karar Osagie Ize-Iyamu, tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP na jihar Edo, Lucky Imasuen, tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Dan Orbih, ciyaman na PDP a Edo, Tony Azigbemi da kuma Efe Erimuoghae Anthony, zuwa ranar 11 ga watan Yuni, 2018.

Ana zargin su da hada kai wurin satar kudaden gwamnatin jihar wanda ya sabawa dokar kasa.

Lauyoyin masu kare wadanda basu halarci kotun ba Dan Orbih, wanda Ferdinard O. Orbih (SAN) ke karewa da kuma Ize-Iyamu, wanda Ikhide Ehighelua ke karewa, sun bayyanawa kotun cewa wadanda suke wakiltar basa gida Najeriya, sun fita kasar waje domin duba lafiyarsu, amma dai zasu gurfana a gaban kotun a zama na gaba.

Kotu ta dage sauraron shariar manyan ‘yan jam’iyyar PDP 5 da ake tuhumar da laifin cin hanci da rashawa

Kotu ta dage sauraron shariar manyan ‘yan jam’iyyar PDP 5 da ake tuhumar da laifin cin hanci da rashawa

A zaman da kotun tayi a ranar Laraba, bata samu damar tuhumar wadanda ake zargin ba sakamakon rashin bayyanar Ize- Iyamu da kuma Dan Orbih a gaban kotun.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Boko Haram sun bulo da wani sabon salo na kai harin kunar bakin wake

Hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta kasa ta gabatar mutanen biyar ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Edo, ne a gaban kotun bisa zargin wasu kudade N700m da suka karba kafin gudanar da zaben 2015.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin hukunta barayin gwamnati komai daren dadewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel