Dalilin da ya sa aka bata lokaci wajen aikin kasafin bana - Bukola Saraki

Dalilin da ya sa aka bata lokaci wajen aikin kasafin bana - Bukola Saraki

- Bukola Saraki ya fadi abin da ya jawo bacin lokaci a aikin kasafin bana

- Shugaban Majalisar dai yace bangaren zartarwa ne su ka bata lokaci

- Har sai da aka kai Watan Maris ba a kare kasafin kudin Ma’aikatu ba

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi jawabi jiya a Majalisa bayan da Shugaban Kwamitin da tayi aikin kasafin kudin bana watau Sanatan Gombe ta tsakiya Mohammed Danjuma Goje ya mika aikin su a gaban 'Yan Majalisar Kasar.

Dalilin da ya sa aka bata lokaci wajen aikin kasafin bana - Bukola Saraki

Saraki yace daga bangaren Gwamnati na MDA aka samu bacin lokaci

Sai jiya ne Allah yayi Majalisun Tarayyar Kasar su ka amince da kasafin kudin 2018 wanda yake hannun su tun farkon Nuwamban bara. Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya bayyana abin da ya sa aikin kasafin kudin ya jima a hannun su.

Shugaban Sanatocin Kasar Bukola Saraki a jawabin na sa ya bayyana cewa akalla fiye da rabin Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Tarayya ba su zo sun kare kasafin kudin su a gaban Majalisar ba lokacin da ake tsakiyar aiki.

KU KARANTA: Akwai wata babbar matsala guda a kasafin bana - Bukola Saraki

Bukola Saraki yace har aka kai karshen Watan Fubrairu amma wasu ba su kare kasafin kudin Ma'aikatun su a gaban Majalisa ba. Idan ba ku manta ba dai sai dai Shugaban Kasa Buhari ya nemi Shugabannin na MDA su hanzarta.

Abubakar Bukola Saraki yace akwai bukatar a samu karin hadin kai tsakanin Majalisa da masu zartarwa domin a rika aiki sumul. A kasafin kudin na bana dai Majalisa tayi kokari wajen ganin an kara ware kudi domin kiwon lafiya a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel